Najeriya

Gobara ta hallaka mutane a Calabar

Gobara ta hallaka mutane a Calabar
Gobara ta hallaka mutane a Calabar

Rahotanni daga garin Calabar da ke jihar Cross Riners a kudancin Najeriya, na cewa sama mutane da 20 sun kwanta dama sakamakon wata gobara da ta tashi a wani gidan mai na Linc Oil da ke unguwar NPA esukutan.

Talla

Wakilinmu a yankin, Musa Kutama, ya rawaito cewa gobara ta tashi ne da misalin karfe 4.20am, bayan wasu mutane da ke satar mai sun fasa bututun da ke kai mai Linc Oil.

Jami’an bada agajin gaggawa sun yi kokarin kashe gobara, yayin da mutane da dama sun kone wasu kuma na gadajen asibiti.

Hukumomin yankin da abin ya auku zuwa yanzu ba su yi karin haske ko bayani kan gobara ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.