Najeriya

Mutane sun mutu a harin bam na Masallacin Maiduguri

Jami'an agajin gaggawa dauke da gawarwakin 'yan kunar bakin waken kauyen Mamanti a jihar Borno ta Najeriya
Jami'an agajin gaggawa dauke da gawarwakin 'yan kunar bakin waken kauyen Mamanti a jihar Borno ta Najeriya Bilyaminu/RFIHausa

Rahotanni daga jihar Borno da ke yankin arewa maso gabashin Najeriya na cewa, wasu ‘yan kunar bakin wake sun tayar da bama-baman da suka yi damara da su a wurare daban, abin da ya yi sanadin mutuwar mutane 8 a Masallacin Maiduguri.

Talla

Wakilinmu Bilyaminu Yusuf ya tabbatar mana da aukuwar lamarin, in da ya ce, da asubahin yau ne wata ‘yar kunar bakin wake ta shiga cikin wani masallaci da ke unguwar London-ciki a birnin Maiduguri kuma ta yi nasarar tayar da bom din da ta yi damara da shi, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 8, yayin da wasu da dama suka jikkata.

Gabanin harin na  yau, wasu ‘yan mata guda biyu sun yi kokarin kashe mutane a kauyen Mamanti da ke jihar a cikin daren da ya gabata, amma wani jami’in tsaro ya bude mu su wuta, abin da ya yi sanadin tarwatsewar bama-baman da suka yi damara da su, kuma nan take suka mutu.

Kungiyar Boko Haram na ci gaba da kai hare-haen kunar bakin wake a wasu sassa na jihar Borno duk da ikirarin murkushe su da sojin kasar suka yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.