Najeriya

Tsoffin gwamnonin Najeriya sun dafe Naira biliyan 40- SERAP

Kungiyar SERAP ta Najeriya ta bukaci Ministan Shari'a, Abubakar Malami da ya gurfanar da tsoffin gwamnonin da suka karbi sama da biliyan 40 a matsayin fansho daga jihohinsu
Kungiyar SERAP ta Najeriya ta bukaci Ministan Shari'a, Abubakar Malami da ya gurfanar da tsoffin gwamnonin da suka karbi sama da biliyan 40 a matsayin fansho daga jihohinsu nigerianpilot.com

Kungiyar SERAP da ke sa ido kan tattalin arzikin al’umma a Najeriya, ta bukaci Ministan shari’a na kasar Abubakar Malami da ya gurfanar da tsoffin gwamnoni da mataimakansu a gaban kotu, domin karbo kudin da suka kai Naira biliyan 40 da suke karba a matsayin fansho daga Jihohinsu duk cewa, a halin yanzu, suna rike da mukaman Sanatoci da Ministoci, in da ake biyan su albashi da alawus-alawus.

Talla

Kungiyar ta ce , tsoffin gwamnonin sun gabatar da doka a gaban Majalisun Jihohinsu kafin barin karagar mulki, wadda ta amince a biya su makudan kudade a matsayin fansho har iya rayuwar su a duniya.

Kungiyar ta ce, wannan doka ta saba ka’ida musamman ganin halin da talakawan kasar ke ciki.

A halin yanzu dai, akasarin gwamnonin na rike da mukaman Sanatoci ko kuma Ministoci a Najeriya.

Kungiyar ta ce, daga cikin tsoffin gwamnonin, akwai Sanata Bukola Saraki na jihar Kwara da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Kabiru Gaya na jihar Kano da Godswill Akpabio na Akwa Ibom, sai Theodore Orji na Abia da Abdullahi Adamu na jihar Nasarawa da Sam Egwu na Ebonyi da kuma Shaaba Lafiagi na Kwara.

Sauran wadanda kungiyar ta ambata sun hada da Joshua Dariye da Jonah Jang na Plateau da Ahmed Sani Yarima na Zamfara da Danjuma Goje na Gombe da Bukar Abba Ibrahim na Yobe da Adamu Aliero na Kebbi da George Akume na Benue da Ms Biodun Olujimi ta Ekiti da Enyinaya Harcourt Abaribe na Abia da Rotimi Amaechi na Rivers da Kayode Fayemi na Ekiti da Chris Ngige na Anambra da kuma Babatunde Fashola na jihar Legas.

Kungiyar ta bukaci Malami da ya yi amfani da kujerarsa ta mai kare muradin jama’a wajen kalubalantar dokar jihohin da ta bai wa tsoffin gwamnonin da a yanzu ke rike da mukamai na Sanatoci da Ministoci damar karbar wasu kudade daga jihohin duk da cewa ana biyan su albashi da alawu-alawus a sabbin mukamansu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.