Bakonmu a Yau

Najeriya: Majalisar dattawa na shirin sauya tsarin fansho.

Sauti 03:33
Wasu tsaffin ma'aikatan gwamnati a Najeriya.
Wasu tsaffin ma'aikatan gwamnati a Najeriya.

Kaduwa da irin wahalar da ma’aikatan da suka yi ritaya ke fuskanta wajen samun kudadensu na fansho, daga kamfanonin tara kudaden, ya sa majalisar Dattawan Najeriya, ta kaddamar da wani shiri na sauya dokar Fanshon da zata taimakawa wadanda suka aje aikinsu. Tuni dai wannan yunkurin ya samu, goyon bayan akasarin ma’aikata da kuma wadanda suka yi ritaya. Dan majalisar dattawa daga jihar Sakkwato, Dr Aliyu Magatakardan Wamakko da ya gabatar da kudirin wanda yanzu haka ya tsallake karatu na biyu, yayi mana bayani akai.