Najeriya: Matan da Boko Haram ta sace sun nemi agajin Gwamnati
Wallafawa ranar:
Kungiyar Boko Haram ta fitar da wani sabon hoton bidiyo, da ke nuna wasu mata da ta sace a jihar Borno.
Matan dai sun roki gwamnatin Najeriya da ta tattauna da mayakan, domin a sako su.
Matan na daga cikin wadanda mayakan Boko na Boko Haram suka sace, yayinda suke kan hanyarsu ta zuwa garin Damboa daga garin Maiduguri a ranar 17 ga watan Yunin da ya gabata, yayinda jami’an tsaro ke musu rakiya.
A lokacin da mayakan sukai wa tawagar motocin kwanton Bauna, sun hallaka wasu daga cikin jami’an tsaron da ake wa rakiya zuwa wuraren aikinsu a garin na Damboa.
Najeriya: Matan da Boko Haram ta sace sun nemi agajin Gwamnati
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu