Najeriya

Babban Hafsan Sojan Najeriya ya bukaci a damke Shekau cikin Kwanaki 40

Janar Tukur Yusuf Buratai Babban Hafsan Sojan Najeriya
Janar Tukur Yusuf Buratai Babban Hafsan Sojan Najeriya rfi

Babban Hafsan sojan Najeriya Tukur Buratai ya dibawa Sojan kasar wa’adin kwanaki 40 da su kamo masa mutumin nan dake ikirarin shine Shugaban Kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau a raye ko a mace.

Talla

Daraktan Hulda da Jama’a na Sojan Najeriya Birgediya Sani Usman Kukasheka ya fadi cikin wata sanarwa cewa Janar Tukur Buratai ya bada wannan umarni ne ga Kwamandan Rundunar Sojan dake fafatawa da Kungiyar Boko Haram Manjo Janar Ibrahim Attahiru.

A can baya,  ansha fadin cewa an kashe Abubakar Shekau amma kuma bayan lokaci kadan sai aji ya fitar da sako da hoton Bidiyo cewa yana raye kuma yana samun nasara.

A lokacin mulkin shugaba Goodluck Jonathan an umarci soja a wancan lokaci da su kama Abubakar Shekau a raye amma kuma har Gwamnatin ta sauka an gaza kama shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI