Najeriya

Buhari ya gana da jiga-jigan jam'iyyar APC a London

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da tawagar Gwamnonin APC a birnin London
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da tawagar Gwamnonin APC a birnin London REUTERS

Wata tawagar manyan kusoshin jam’iyyar APC da ta kunshi gwamnonin jihohi daga jam’iyyar, ta gana da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari wanda ke jinya yanzu haka a birnin London.

Talla

A cikin wadanda suka gana da shugaban akwai gwamnan Imo Rochas Okorocha, sai Umaru Tanko Almakura na Nasarawa, da Nasir El-Rufai na Kaduna, da kuma Yahya Bello na jihar Kogi, sai kuma John Oyegun shugaban jam’iyyar APC na kasa.

Gwamnan jihar Nasara Umaru Tanko Almakura, ya shaida wa sashen hausa na RFI cewa, sun samu shugaba Buhari a cikin kyakkawan yanayi, kuma sun ci abinci tare baya ga daukan tsawon lokaci suna hira cikin raha.

Almakura ya kara da cewa, shugaba Buhari ya samu lafiya ta yadda zai iya komawa kasarsa nan ba da jimawa ba don ci gaba da jagorancin Najeriya.

Sai dai Almakura bai sanar da hakikanin ranar da Buhari zai koma gida ba.

Ziyarar da jiga-jigan jam’iyyar ta APC mai mulki ta kai wa shugaban, na zuwa ne bayan wadda mukaddashin shugaban kasar, Yemi Osinbajo ya kai a ‘yan kwanakin nan.

Har yanzu dai, babu cikakken bayani dangane da ainihin larurar da Buhari ke fama da ita, yayin da ‘yan kasar ke ci gaba da cece-kuce kan rashin lafiyarsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.