Isa ga babban shafi
Najeriya

‘’Najeriya ba ta da shirin kara yawan man da ta ke hakowa’’

Sakatare Janar na kungiyar OPEC Mohammed Barkindo
Sakatare Janar na kungiyar OPEC Mohammed Barkindo PIUS UTOMI EKPEI / AFP
Zubin rubutu: Umaymah Sani Abdulmumin
Minti 1

Kungiyar Kasashe masu arzikin man fetur ta duniya, OPEC, ta ce Najeriya ba ta da shirin kara yawan man da ta ke hakowa yanzu haka.

Talla

Sakatare Janar na kungiyar Mohammed Barkindo ya ce Najeriya na fitar da ganga miliyan guda da 800,000 ne kowacce rana, sabanin ganga sama da miliyan biyu da aka santa da shi.

Jami’in ya ce Najeriya zata ci gaba da fitar da wannan adadi har zuwa karshen watan Maris na shekara mai zuwa.

Barkindo ya kuma ce Libya za ta ci gaba da fitar da ganga miliyan guda da 250,000.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.