Najeriya-Boko Haram

Osinbajo ya umarci Burutai ya koma Maiduguri

Babban Hafsan sojin Najeriya Laftanal Janar Tukur Yusuf Buratai
Babban Hafsan sojin Najeriya Laftanal Janar Tukur Yusuf Buratai thenewsnigeria

Mukaddashin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo ya umarci babban Hafson rundunar sojin kasa Laftanal Janar Tukur Burutai da na sojin sama Sadiq Abubakar su koma birnin Maiduguri na jihar Borno da ke yankin arewa maso gabashin kasar don magance matsalar tsaron da ake ci gaba da fuskanta.

Talla

Matakin dai ya biyo bayan ganawar da shugaban ya yi da hafsoshin tsaron kasar biyu kan harin da mayakan Boko haram suka kaddamar jiya wanda ya yi sanadin mutuwar wani Kaftin din soja da wasu mutum 9 ciki har da malaman jami'ar Maiduguri.

Bayan harin na jiya ma dai, a baya-bayan nan kungiyar ta Boko haram ta kaddamar da sabbin hare-hare da dama a jihar ta Borno wadda dama ayyukan kungiyar suka yi kamari a cikinta.

tun bayan rantsar da gwamnati mai ci ta shugaban kasar Muhammadu Buhari ya sanar da mayar da Ofishin bayar da umarnin yaki zuwa Maiduguri daga birnin tarayyar kasar Abuja, lamarin da ake ganin ya taimaka wajen kakkabe mayakan kungiyar ta Boko haram baya ga samun nasarar kwace wasu muhimmman yankuna da suka karbe iko da su a jihar ta Borno.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.