Boko Haram ta Kashe Mutane 69 a Kwanton Bauna Yayin da Ta Fitar Da Sabon Bidiyo Na Mutane Uku Da Ta Kama
Wallafawa ranar:
Kungiyar Boko Haram a Najeriya ta fitar da hoton bidiyo dake nuna wasu mutane uku dake cikin ayarin kwararrun albarkatun karkashin kasa daga Jami'ar Maiduguri da ta kama take garkuwa da su tun Talata a lokacin da ayarinsu da rakiyar soja ke ziyara a arewacin Borno.
Hoton Bidiyon na mintoci hudu na nuna mutane hudu na bayyana kansu da matsayinsu a Jamiar Maiduguri suna rokon hukumomin Najeriya da su biyawa masu jihadin bukatunsu.
An bayyana cewa masu jihadi dake bangaren Abu Mus’ab Al-Barnawi masu samun goyon bayan kungiyar IS ke garkuwa da su.
Majiyoyi dai sun shaidawa kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP cewa mutane kusan 69 aka kashe yayin harin kwanton bauna da mayakan Boko Haram suka kaiwa ayarin kwararrun dake samun rakiyar soja domin binciken albarkatun man fetur a yankin arewa maso gabashin Borno.
Ana ganin yawan mutane da kungiyar ta kashe a tashi guda wannan karo na daga cikin mafi muni dan tsakanin nan.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu