Najeriya

Jami'ar Maiduguri ta caccaki sojin Najeriya

Shugaban rundunar sojin Najeriya, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai.
Shugaban rundunar sojin Najeriya, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai. thenewsnigeria

Shugaban Jami’ar Maiduguri da ke jihar Borno ta Najeriya, Abubakar Njodi ya caccaki rundunar sojin kasar bisa ikirarinta na ceto ma’aikatan hakar man fetir da mayakan Boko Haram suka yi wa kwanton- bauna.

Talla

Njodi ya ce, har yanzu ya gaza fahimtar dalilin da ke sa rundunar sojin Najeriya ke yada labaran jabu.

Wannan na zuwa ne bayan rundunar sojin ta ce, ta ceto dukkanin manazarta kimiyyar kasa na jami’ar Maiduguri da ke aiki da kamfanin mai na NNPC.

A cewar Njodi, jami’ar ta Maiduguri ta yi rashin zaratan malamai hudu a sashen kimiyyar kasa sakamakon farmakin na Boko Haram, kuma ya ce, babu wanda ya yi kasa da shekara 10 a cikinsu yana karantawar, abin da ya bayyana da babbar asara ga jami’ar.

"Mawuyaci ne a gare ni na samu wadanda za su maye guraben wadannan malamai da muka yi rashinsu." in ji shugaban Jami'ar.

Njodi ya bayyana cewa, gano gawarwakin da sojin suka yi, ba ya nufin ceto manazartan.

Boko Haram ta dirar wa tawagar masana kimiyar kasar ne da wasu jami’an tsaro akan hanyarsu ta zuwa aikin gano man fetir a karkashin jagorancin kamfanin NNPC a yankin tafkin chadi.

Wasu rahotanni na cewa, kimanin mutane 40 ne suka mutu da suka hada da jami'an tsaro a dalilin farmakin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.