Najeriya

An saki daliban da aka yi garkuwa da su a Legas

Daliban da aka wasu 'yan bindida suka yi garkuwa da su a jihar Legas ta Najeriya
Daliban da aka wasu 'yan bindida suka yi garkuwa da su a jihar Legas ta Najeriya punchng.com

An saki dalibai 6 na wata makaranta da ke jihar Legas a kudancin Najeriya bayan sun shafe sama da watanni biyu a hannun mutanen da suka yi garkuwa da su don karbar kudin fansa.

Talla

Rahotanni sun ce, an saki daliban ne na makarantar Igbonla Model College bayan an sake biyan masu garkuwa da su Naira miliyan biyar a matsayin kudin fansa.

Wata majiyar tsaro ta ce, jumullar Naira miliyan 37 aka biya don ‘yanto daliban daga hannun mutanen.

A ranar 25 ga watan Mayun da ya gabata ne, wasu ‘yan bindiga sanye da kakin soji suka dirar wa makarantar, in da suka sace daliban daga dakin kwanansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.