Najeriya

Sojan Sama A Najeriya Ta Tura Naurorin Hangen Nesa Borno Don Hango 'Yan Kunar Bakin Wake

Babban Hafsan sojan Najeriya  Tukur Yusuf Buratai
Babban Hafsan sojan Najeriya Tukur Yusuf Buratai RFI

Rahotanni daga jihar Borno a Nigeria na cewa mutane akalla 8 ne suka gamu da ajalinsu wasu 15 kuma suka jikkata sakamakon harin kunar bakin wake a wasu rukunin gidaje a garin Dikwa mai tazaran kilomita 80 daga birnin Maiduguri.

Talla

Wannan hari na zuwa ne a daidai wani lokaci da Rundunar Sojan Sama ke sanar da tura Naurorin hangen nesa yankin arewa maso gaba domin taimakawa jamian tsaro bankado hare-haren kunar bakin wake kafin su auku.

Rahotannin na nuna tun ajiya ne da yamma aka kai  hari sabon harin kunar bakin wake, kuma wasu 'yan mata biyu suka kai wannan hari.

Tun a shekara ta 2015 sojan Nigeria suka sake kwace garin Dikwa daga hannun kungiyar Boko Haram.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.