Najeriya

Kungiyar 'yan jaridu ta bukaci a bi mata hakkinta a Kaduna

Kungiyar 'yan Jaridu a Najeriya reshan Jihar Kaduna ta bukaci a bi mata hakkinta kan raunata wasu manema labarai
Kungiyar 'yan Jaridu a Najeriya reshan Jihar Kaduna ta bukaci a bi mata hakkinta kan raunata wasu manema labarai http://www.nujnig.org/

Kungiyar 'yan Jaridu ta Najeriya reshen Kaduna ta bai wa rundunar 'yan sandar jihar wa'adin makonni biyu ta gudanar da sahihin bincike tare da hukunta jami'inta.

Talla

Bukatar ya biyo bayan zargin da ake wa jami’an da taimakawa 'yan bangar siyasa wajen tada rikicin a lokacin taron manema labarai da wasu jiga-jigan jam'iyyar APC a jihar suka kira domin nuna rashin gamsuwar su da zaben wakilan jam'iyyar zuwa babban taron ta na kasa.

Cikin wadanda suka halarci taron sun hada da sanata Suleman Hunkuyi da Sanata Shehu Sani da kuma Isah Ashiru kudan.

A saurare karin bayani a Rahoton da wakilinmu na Kaduna Aminu Sani Sado ya aiko mana.

Kungiyar 'yan jaridu ta bukaci a bi mata hakkinta a Kaduna

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI