Najeriya

Kura Ta Lafa A Kano Bayan Hargitsi Tsakanin Kwankwasiya Da Gandujiya

Gwamnan jihar Kano  Abdullahi Umar Ganduje tare da wakilin sashen Hausa na RFI a Kano Abubakar Dandago
Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje tare da wakilin sashen Hausa na RFI a Kano Abubakar Dandago RFIHausa/Dandago

Rahotanni daga jihar Kano a Najeriya na cewa kura ta lafa bayan kazamin yamutsi da aka samu tsakani magoya bayan tsohon Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso da ake kira ‘yan Kwankwasiya da kuma magoya bayan Gwamna mai ci  Dr Abdullahi Ganduje da ake kira ‘yan Gandujiya.

Talla

Mutane biyu da suka sami munanan raunuka wato tsohon Sakataren Gwamnati karkashin Gwamna Kwankwaso wato Rabiu Bichi da wani kani na  tsohon Gwamna mai suna Sani na samun sauki a asibiti.

Majiyoyin samun labarai na cewa jami'an ‘yan sanda na gudanar da cikakken binciken lamarin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.