Najeriya

Ya kamata Buhari ya rika mutunta ni-Patience Jonathan

Uwargida Patience Jonathan
Uwargida Patience Jonathan

Uwargidan tsohon shugaban Najeriya, Patience Jonathan ta bukaci shugaba Muhammadu Buhari da ya rika mutunta ta kamar yadda mai gidanta ke mutunta A’isha Buhari bayan kayin da suka sha a zaben 2011.

Talla

Patience Jonathan ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin, in da kuma ta koka kan yadda hukumar yaki da cin hanci da rashwa, EFCC ta sanya ta a gaba saboda zargin al’mundahana.

Mrs. Jonathan ta ce, hukumar EFCC na binciken ta ne saboda rawar da ta taka a lokacin shirye-shiryen zaben 2015 da ya kawo karshen mulkinsu a karkashin jam’iyyar PDP.

Gabanin gudanar da zaben dai, Patience Jonathan ta bayyana shugaba Buhari a matsayin mutum mai raunin kwakwaluwa.

Uwargidan ta kara da cewa, abin da ya faru a lokacin yakin neman zaben, bai kamata ya zama silar musguna ma ta ba a yanzu.

Har ila yau, Patience Jonathan ta bukaci Buhari da ya ja kunnen mukaddashin shuganam hukumar EFCC, Ibrahim Magu da ta ce, ya fito ne don ganin bayan iyalinta.

A cewar Patience, ya kamata Buhari ya dauki darasi daga salon shugabancin Donald Trump na Amurka, wanda ta ce, bai damu da sha’anin uwargidan Barack Obama ba da ya mika ma shi mulki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.