Najeriya

Majalisar ta kaddamar da bincike kan shugaban NNPC a Najeriya

Ofishin Kamfanin Mai na NNPC a Najeriya
Ofishin Kamfanin Mai na NNPC a Najeriya REUTERS/Afolabi Sotunde

Majalisar Dattawan Najeriya ta kafa wani kwamiti na musamman da zai gudanar da binciken zargin zagon kasa da cin hancin da ake yiwa shugaban kamfanin man kasar, NNPC, Maikanti Baru.

Talla

Wasikar da aka tseguntawa Manema labarai ta bayyana cewar Baru na yi wa Ministan zagon kasa da kuma bada manyan kwangiloli da dibar manyan ma’aikata ba tare da ya gabatar masa ko kuma hukumar gudanarwar kamfanin ba.

Wannan batu da ke daukan hankula al'ummar kasar akwai yiwuwar shugaban kasar Muhammadu Buhari ya gana da Ministan yau alhamis, kamar yadda wasu majiyoyi suka rawaito.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.