Najeriya

Najeriya ta ce babu bukatar dawo da Diezani

Tsohuwar Ministar Mai Diezani Allison-Madueke
Tsohuwar Ministar Mai Diezani Allison-Madueke AFP / Wole Emmanuel

Gwamnatin Najeriya ta ce babu dalilin bukatar dawo da tsohuwar ministan man fetur Diezani Allison Madukwe daga Burtaniya domin fuskantar shari’a a kasar

Talla

Ministan shari’a Abubakar Malami ya ce babu dalilin bukatar dawo da tsohuwar ministan gida tunda acan ma tana fuskantar wata shari’a na mallakar wani gida da kudin sa ya kai Fam miliyan 10.

Ita dai Diezani ta bukaci gwamnatin Najeriya ta bukaci a bata izinin komawa gida ne domin shiga wata shari’a ta dabam wadda ta shafi wasu jami’an ta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.