Najeriya ta samu gurbi a gasar kofin duniya a Rasha
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Sauti 10:00
Shirin duniyar wasanni na wannan makon tare da Abdurrahman Gambo Ahmad ya tattauna ne game da nasarar da Najeriya ta kan Zambia da ci 1-0 a birnin Uyo, abin da ya bai wa Super Eagles damar zuwa gasar cin kofin duniya da za a gudanar a shekara mai zuwa a Rasha. Shirin ya yi nazari kan abubuwan da suka taimaka har Najeriya ta kai ga gaci, yayin da wasu suka bayyana bacin ransu kan jinkirin da aka samu kafin Najeriyar ta zura kwallonta ta hannun Alex Iwobi a minti na 73.