Bakonmu a Yau

Dakta Haruna Yarima kan tsarin ayyuka a Najeriya

Sauti 03:13
Shugaba Muhammadu Buhari da majalisar ministocinsa
Shugaba Muhammadu Buhari da majalisar ministocinsa résidence nigériane

Wata takaddama ta kaure a Najeriya tsakanin al’ummomin kasar kan bayanin da shugaban Bankin Duniya Jim Yong Kim ya yi cewar shugaban kasar Muhammadu Buhari, ya bukace su da su karkata akalar ayyukan su zuwa Yankin Arewa Maso Gabas sakamakon ta’adin da kungiyar Boko Haram ta yi. Dangane da wannan, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Dakta Haruna Yarima, tsohon Dan Majalisa, malamin Jami’a kuma wanda ya fito daga Yankin, kuma ga abinda ya ke cewa a kai.