Najeriya- MDD

Najeriya ta sake bukatar kujera a MDD

Shugaban kasar Najeriya Mohammadu Buhari
Shugaban kasar Najeriya Mohammadu Buhari Sunday AGHAEZE / NIGERIA STATE HOUSE / AFP

Najeriya ta sake gabatar da bukatar ta na sake takarar kujera a Hukumar kare Hakkin Bil Adama ta Majalisar Dinkin Duniya yayin da wa’adin ta na shekaru biyu ke shirin karewa.

Talla

Jakadan Najeriya na din-din-din a Majalisar Audu Kadiri ya ce tuni gwamnatin Najeriya ta gabatar da takarar ta domin ci gaba da zama a Majalisar tsakanin shekarar 2018 zuwa 2020.

Idan ta yi nasara, Najeriya zata zama kasa ta 4 daga Afirka ta Yamma da ke da kujera a Majalisar, kuma kasa ta 13 daga Afirka a Majalisar mai wakilai 47.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.