Najeriya

Buhari ya umarci sojoji da 'yan sanda su tashi tsaye kan tsaron Filato

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. REUTERS/Kevin Lamarque

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya umurci sojoji da Yan Sandan kasar da su tabbatar da samar da cikaken tsaro a Jihar Filato sakamakon wani kazamin harin da ya lakume rayukan mutane 27.

Talla

Wata sanarwar da kakakin shugaban, Garba Shehu ya rabawa manema labarai, ta ce shugaba Buhari ya kadu sosai da munanan hare haren da ake samu a Jihar ta Filato.

Shugaban ‘yan Kabilar Irigwe Sunday Audu yace garuruwa 7 aka kai wa hari cikin wata guda aka kuma kashe mutane 41.

Sai dai yayin Karin hasken da ya yiwa Sashin Hausa na RFI, Lumumba Dah Ade, daya daga cikin shugabannin al’umma a yankin yace da alama jami’an tsaro basa gayawa shugaba Buhari gaskiyar abinda ke faruwa.

Buhari ya umarci sojoji da 'yan sanda su tashi tsaye kan tsaron Filato

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.