Najeriya

Buhari ya umarci a kori Abdurasheed Maina

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari REUTERS/Kevin Lamarque

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bada umurnin gagauta sallamar Abdurasheed Maina daga aikin gwamnati bayan korafe-korafen da suka biyo bayan mayar da shi aiki da kuma kara masa girma.

Talla

Mai taimakawa shugaban kan harkokin yada labarai Femi Adeshina ya ce shugaba Buhari ya kuma bukaci gabatar masa da rahoto kan matakan da ka bi wajen mayar da shi aiki da kuma kara masa girma kafin tashi daga aiki yau.

'Yan Najeriya da dama da kungiyoyin da ke yaki da cin hanci da rashawa sun bayyana shakku kan yaki da cin hanci da gwamnatin ke ikrarin yi ganin yadda aka mayar da Maina aiki.

Rahotanni da sharhi kan gwamnatin Muhammadu Buhari
Shugaban Kasar Najeriya Muhammadu Buhari Sunday AGHAEZE / NIGERIA STATE HOUSE / AFP

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.