Najeriya

A gabatar da Jonathan a Kotu- Olisa Metuh

Tsohon shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan
Tsohon shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan REUTERS/Afolabi Sotunde

Tsohon kakakin jam’iyyar PDP mai adawa a Najeriya Olisa Metuh, ya bukaci a gabatar da tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan a gaban kotu domin ya bayar da shaida dangane da zargin rashawa da ake yi masa.

Talla

Metuh ya bayyana hakan ne a gaban kotu da ke Abuja inda ake zarginsa da Rashawa.

Hukumar yaki da rashawa ta EFCC ce ta gurfanar da Metuh kan zarginsa da hannu a badakalar kudaden da yawansu ya kai Naira milyan 400 daga kudaden makamai na hannun tsohon mai bai wa shugaban shawara kan harkokin tsaro Sambo Dasuki.

Mista Metuh ya ce dole sai an gabatar da Jonathan gaban kotun domin warware zare da abawa kan batun.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.