Najeriya

Najeriya za ta karbi bakuncin gasar ninkaya ta Afrika

Ana sa ran fara gasar wasannin ninkayar daga 27 zuwa 29 ga watan da muke ciki na Oktoba.
Ana sa ran fara gasar wasannin ninkayar daga 27 zuwa 29 ga watan da muke ciki na Oktoba. http://thenewsnigeria.com.ng

Najeriya za ta karbi bakoncin gasar wasannin ninkaya na yammacin Afrika da zai gudana daga 27 zuwa 29 ga watan Oktoban da muke ciki.

Talla

Fiye da kasashe 20 ne ake sa ran za su halarci a wasan a najeriyar, daga yankunan tsakiya da yammacin Afrika, inda tuni hukumomin kula da wasannin ninkaya na kasar suka bayar da tabbacin cewa sun kammala shiryawa tsaf don tunkarar wasannin.

Rahotanni sun ce kawo yanzu an gudanar da wasu gyare-gyare a filin wasan ninkaya na kasar da ke Lagos.

Filin wasannin ninkayan dai shi ne wanda ya karbi bakoncin wasannin ilahirin nahiyar Afrika a shekarar 1973 a don haka ake ganin yana da girman da zai iya daukar kasashen 20 a wannan karon.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.