Najeriya-Boko Haram

Sojin saman Najeriya sun hallaka mai dakin Shekau

Jagoran kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau.
Jagoran kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau. News Ghana

Rundunar sojin Saman Najeriya ta ce akwai yiwuwar ta yi nasarar hallaka mai dakin jagoran kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau yayin luguden wutar da dakarun Operation ruwan wuta suka yi a maboyar mayakan da ke Durwawa cikin karamar hukumar Konduga a jihar Borno.

Talla

Sanarwar da Rundunar ta fitar a yau dauke da sa hannun kakakinta Air Commadore Adetokunbo Olasanya ta ce, dakarunta na Operation ruwan wuta da aka kaddamar a baya-bayan nan za su ci gaba da kai sumame maboyar mayakan don ci gaba da kakkabe burbushinsu daga Najeriyar.

Rundunar ta ce dakarun sun hallaka mayakan Boko Haram da dama, lamarin da ya sa ta ke kyautata zaton cikin wadanda aka hallaka har da Maidakin Shekau.

Kakakin Rundunar Air Commadore Adetokunbo Olasanya ya tabbatar da harin yana mai cewa sun shammaci mayakan ne a lokacin da su ke tsaka da wani taro karkashin jagorancin Matar Shekau da aka bayyana Sunanta da Fiddausi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.