Najeriya

Salami ya yi watsi da nadin da aka yi masa

Justice Ayo Salami na Najeriya
Justice Ayo Salami na Najeriya THISDAYLIVE.COM

Tsohon Shugaban kotun daukaka karar a Najeriya, Ayo Salami ya ki karbar nadin da aka masa na jagorancin wani kwamiti da zai sanya ido kan alkalan da ke shari’ar cin hanci da rashawa da kuma tabbatar da ba’a samun tsaiko wajen gudanar da shari’ar.

Talla

Daraktan yada labaran Hukumar da ke kula da ayyukan shari’a Soji Oye, ya tabbatar da kin amincewar Mai Shari’a Salami na karbar aikin, sai dai bai yi Karin bayani kan dalilin daukar matakin ba.

Shugaban alkalan Najeriya Waltaer Onnoghen ya nada Salami wannan mukami a yunkurin sa na tsaftace ayyukan shari’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.