Najeriya

Najeriya ce ke dauke da kashi 20 na haihuwar yara a Afrika - UNICEF

Nahiyar Afrika zata zarta turai samun yawaitar haihuwa a karshen karni.
Nahiyar Afrika zata zarta turai samun yawaitar haihuwa a karshen karni. AFP/File

Asusun kula da yara kanana na Majalisar Dinkin duniya UNICEF, ya ce kashi 20 cikin 100 na haihuwar kananan yara a duniya na aukuwa ne a Najeriya.

Talla

UNICEF ta bayyana haka ne, cikin rahoton da ta wallafa mai taken "Yadda al’ummar nahiyar Afrika ka iya kasancewa a shekara ta 2030".

Rahoton ya yi hasashen cewa nan da shekara ta 2050 mai zuwa, cikin kowace haihuwa 13 da za’a samu a duniya, za’a rika samun guda a Najeriya, dan haka tilas a kara kaimi, wajen ware makudan kudaden da zasu bada damar samar da cikakkiyar kulawa ga kananan yara a nahiyar Afrika.

UNICEF ta kara da cewa tilas a bai wa Najeriya muhimmanci, idan aka yi la’akari da yadda hasashe ya nuna cewa, nan da zuwa shekara ta 2030, za’a haifi yara miliyan 120 a Najeriya kadai, adadin da zai zarta na dukkanin haihuwar da za’a samu a nahiyar turai baki daya, yayinda Najeriyar zata kwashe kashi 6 na haihuwar da ake samu a fadin duniya.

A shekarar 1950 nahiyar Afrika ke da kashi 10, na kananan yara da ke duniya, sai dai hasashen hukumar UNICEF ya ce idan aka cigaba da samun yawaitar haihuwa a nahiyar zuwa shekara ta 2100, kashi 50 na kananan yara da ke rayuwa a duniya zasu fito ne daga nahiyar Afrika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI