Najeriya

Buhari zai fadada majalisar ministocinsa

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari REUTERS/Afolabi Sotunde

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana shirin fadada Majalisar ministocinsa domin sanya sabbin mutanen da ke dauke da sabbin dabarun yadda za a inganta kasar da kuma samar mata da ci gaba.

Talla

Buhari ya bayyana haka ne wajen taron shugabannin Jam'iyyar APC da aka gudanar wannan talata a Abuja, kuma matakin na zuwa ne a dai-dai lokacin da 'yan Najeriya da dama ke bukatar ganin shugaban ya yi garambawul ga daukacin Majalisar domin kawar da ministocin da basa tabuka komai wajen yiwa talakawa aiki.

Shugaban ya kuma nemi gafara kan jinkirin da aka samu wajen rashin kammala nade-naden shugabanin gudanarwar hukumomin gwamnati da dama.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.