Tsarin biyan tukwici ga masu fallasa kudaden sata dai dai ne - Ribadu

Sauti 03:41
Tsohon shugaban hukumar EFCC Malam Nuhu Ribadu.
Tsohon shugaban hukumar EFCC Malam Nuhu Ribadu. The Whistler

Tsohon Shugaban Hukumar EFCC, Nuhu Ribadu, ya yaba da matakin da Gwamnatin Najeriya ta dauka, na bada tukuici ga mutanen da suka fallasa barayin gwamnati domin kwato dukiyar jama’a. Yayin da yake jawabi wajen wani taro kan yaki da cin hanci da rashawa a Abuja, Ribadu yace samun irin wadannan bayanai daga jama’a ya taimaka masa sosai wajen gano kudaden sata a lokacin da ya jagoranci hukumar EFCC. Ga dai abinda Nuhu Ribadu ya shaida mana yayin tattaunawarsa da Bashir Ibrahim Idris.