Najeriya

Ba mu yi sakaci da harkar tsaro ba- Gwamnatin Zamfara

Gwamnan jihar Zamfara Abdul'aziz Yari.
Gwamnan jihar Zamfara Abdul'aziz Yari. RFI-HAUSA

Gwamanatin Jihar Zamfara a Najeriya ta yi watsi da zargin da ake yi ma ta na yin sakaci game da kare rayukan fararen hula bayan wani kazamin hari da wasu ‘yan bindiga suka kai a karamar hukumar shinkafi, inda suka kashe mutane sama da 50.

Talla

Masu rajin kare hakkin bil’adama a jihar sun yi barazanar shigar da kasar gwamnatrin jihar a kotu saboda zargin gazawa wajen kare rayukan jama’a.

Mai taimaka wa gwamnan jihar Zamfara kan harkar tsaro Ibrahim Dosara ya ce ba gaskiya ba ne kalaman da ake cewa gwamnatin jihar tana sakaci a kan al’amarin.

Ya ce matsalar tsaro al’amari ne da ya shafi yankuna daban-daban na cikin kasa, kuma gwamnatin jihar a nata bangaren tana iyakar bakin kokarinta wajen ganin ta shawo kan matsalar.

Dosara ya ce gwamnati na kokarin hada kai da al'umma domin ganin an magance wadannan hare-hare da ake kaiwa a wasu yankuna na jihar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.