Mahara sun hallaka mutane 30 a Numan

Wasu mahara sun hallaka mata da kananan yara 30 a yankunan Fulani da ke karamar huhkumar Numan da ke jihar Adamawa.
Wasu mahara sun hallaka mata da kananan yara 30 a yankunan Fulani da ke karamar huhkumar Numan da ke jihar Adamawa. guardian.ng

Akalla mata da kananan yara 30 ne aka hallaka a karamar hukumar Numan da ke jihar Adamawa, a arewa maso gabashin Najeriya.

Talla

Rundunar ‘yan sandan jihar da kuma shaidun gani da ido sun ce, gungun maharani da ake kyautata zaton sun fito ne daga kabilar Bachama sun afka ne kan yankunan da Fulani ke zama.

Kauyukan da hare-haren suka shafa sun hada da Shafaran, Shawal, Gumara, Kikam, da kuma Kadamti.

Ko da yake kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ta Adamawa, usman Abubakar ya tabbatar da cewa mutane 30 maharan suka hallaka a jiya Litinin, akwai fargabar mai yiwuwa yawan mamatan ya zarta hakan nan gaba.

A ranar Talata mataimakin gwamnan Jihar Martins Babale, ya ziyarci wadanda harin ya shafa, inda ya sha alwashin zakulo wadanda ke da hannu.

Labarin harin na karamar hukumar Numan ya zo ne a daidai lokacin da al’ummar jihar ta Adamawa ke murmurewa daga harin dan kunar bakin waken da ya hallaka mutane 50 a wani Masallaci da ke garin Mubi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.