Najeriya

Sojin Najeriya za su kware a Hausa da Yarbanci cikin shekara guda

Shugaban rundunar sojin Najeriya Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai.
Shugaban rundunar sojin Najeriya Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai. thenewsnigeria

Rundunar sojin Najeriya ta bai wa dukkanin jami’anta umarnin fara koyan manyan harsunan kasar wato, Hausa da Yarbanci da yaran Igbo.

Talla

Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ya fitar a safiyar yau Laraba Birgediya Janar Sani Usman Kuka Sheka ta ce, ana saran dukkanin jami’an su kware a manyan harsunan nan da watan Disamban shekarar 2018.

Kuka Sheka y  ce, umarnin na cikin sabon tsarin koyan harsuna da rundunar sojin ta bullo da shi.

Sanarwar ta ce, sabon tsarin zai taimaka wa sojojin ta fannin huldar sadarwa da sauran al’ummar, sannan kuma zai taka rawa wajen tattara bayanai.

A cewar sanarwar, kwarewa a harsunan uku za ta bai wa masu neman shiga aikin soji a kasar wani fifiko na musamman wajen daukan aiki.

Kafin wannan sabon tsarin dai, rundunar sojin ta bukaci jami’anta da su koyi Faransanci da Larabci da Spaniyanci da yaran Portuguese da kuma Swahili.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.