Najeriya

Najeriya: Za'a kafa cibiyoyin 'yan sanda na musamman a Adamawa

Ibrahim Idris, Inspector General of Nigeria Police
Ibrahim Idris, Inspector General of Nigeria Police independent.ng

Sifeto janar na ‘yan sandan Najeriya, Ibrahim Idris, ya ce rundunar zata kafa cibiyoyin jami’an ‘yan sanda na musamman guda 5, domin magance matsalar rikici tsakanin manoma da makiyaya.

Talla

Sifeton ya bayyana matakin da zasu dauka ne, a lokacin da ya ziyarci gwamnan jihar ta Adamawa Jibrila Bindow, domin nuna alhini bisa harin da ya hallaka mata da yara a Numan.

Mista Ibrahim yace cibiyoyin zasu kasance cikin shirin ko ta kwana, domin samun kai wa ga dukkanin wuraren da suka samu rahoton bullar barazanar tsaro cikin gaggawa.

Matakin rundunar ‘yan sandan ya zo ne bayanda a ranar Litinin wasu mahara suka hallaka mata da kananan yara na Fulani akalla 60 a karamar hukumar Numan da ke jihar Adamawa.

Bayan harin ne kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN, ya rawauto cewa an samu arrangama tsakanin Fulani makiyaya da wasu manoma a dai karamar hukumar ta Numan, lamarin da ya kai ga jikkatar akalla mutane 20.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.