Adamawa

An kara daukar matakan tsaro a Numan - SP Abubakar

'Yan bindiga sun hallaka jami'an 'yan sanda 4 a karamar hukumar Numan da ke jihar Adamawa.
'Yan bindiga sun hallaka jami'an 'yan sanda 4 a karamar hukumar Numan da ke jihar Adamawa. Frontiers News

Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa, ta tabbatar da mutuwar jami’anta hudu a musayar wuta da suka yi, da wasu ‘yan bindiga a karamar hukumar Numan.

Talla

Kakakin rundunar SP Usman Abubakar, ya ce har yanzu basu kai ga gano, ku su waye ‘yan bindigar ba.

Harin ya jefa tsoro cikin zukatan mazauna yankin, lamarin da ya tilastawa da dama tserewa zuwa wasu wuraren, don kaucewa abinda zai iya biyo baya.

SP Abubakar ya ce babu gaskiya cikin jita-jitar cewa ‘yan bindigar Fulani ne da suke kokarin daukar fansa bisa kashe musu mata da kanan yara da aka yi a watan da ya gabata, bincike ne kawai zai tabbatar da ko su wayen maharan.

Kakakin ‘yan sandan, ya kuma bukaci jama’a da su kwantar da hankulansu, kasancewar an kara yawan jami’an tsaro a karamar hukumar domin tabbatar da doka da oda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI