Najeriya

An nada sabon kwamandan yaki da Boko Haram a Najeriya

Sojojin Najeriya na ci gaba da kokari kakkabe mayakan Boko Haram a yankin arewa maso gabashin kasar
Sojojin Najeriya na ci gaba da kokari kakkabe mayakan Boko Haram a yankin arewa maso gabashin kasar REUTERS/Stringer

Gwamnatin Najeriya ta nada sabon kwamandan rundunar sojin da ke yaki da kungiyar Boko Haram da akafi sani da rundunar zaman lafiya dole da ke da cibiya a  Maiduguri.Daraktan yada labaran rundunar sojin kasar Janar Sani Usman Kukasheka yace an nada Manjo Janar Rogers Ibe Nicholas domin maye gurbin Manjo Janar Ibrahim Attahiru.

Talla

Sanarwar na zuwa ne a wani lokaci da sojojin Najeriya ke kokarin magance hare- haren mummuke da ake samu daga mayakan Boko Haram bayan sojojin da gwamnati sun bayyana samun nasara akan su.

Bayanai daga Jihohin Adamawa da Borno sun nuna cewar, an samu wasu hare- haren kunar bakin wake a Mubi da Madagali da Biu, abin da ya haddasa asarar rayuka.

Sai dai rundunar sojin ba ta yi bayani kan dalilin sauya manyan hafsoshin ba, in da ta ke cewa matakin na daga cikin sauyin da ake samu lokaci zuwa lokaci.

Daraktan yada labaran Janar Kukasheka ya ce, sabon kwamandan, Janar Rogers ya fito ne daga shalkwatan sojin da ke Abuja, yayin da Janar Attahiru zai koma can in da zai yi aiki a sashen tsare-tsaren manufofin rundunar sojin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.