Najeriya

Najeriya ta ɓullo da shirin magance rikicin Manoma da Makiyaya

Rikicin Fulani da Makiyaya na haddasa asarar rayuka a Najeriya
Rikicin Fulani da Makiyaya na haddasa asarar rayuka a Najeriya guardian.ng

Gwamatin Najeriya ta ƙaddamar da wani shiri na lalubo hanyar magance tashin hankalin da ke haddasa asarar rayuka tsakanin Fulani makiyaya da manoma a ƙasar.

Talla

Mai Magana da yawun mataimakin shugaban ƙasar Laolu Akande ya ce, Farfesa Yemi Osibanjo ya gana da wasu manyan Sarakunan arewacin ƙasar da suka haɗa da Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II da Lamidon Adamawa Muhammad Barkindo Mustapha kan yadda za a kawo karshen wannan rikici.

Baba Ngelzerma, Sakataren kungiyar Fulai ta Myetti Allah da ya halarci taron na jiya Litinin, ya shaida wa sashen hausa na RFI cewa, baya ga batun rikicin Fulani da makiya, tattaunawarsu ta kuma mayar da hankali kan yadda za a samar da zaman lafiya mai ɗorewa a Najeriya

Osinbajo da ya kai ziyara Numan da ke Adamawa don ganewa idanusa irin barnar da rikicin ya haifar a makon jiya, ya ce, gwamnatin tarayya za ta samar da dawwamammiyar hanyar magance rikicin a sassan Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI