Najeriya

Dan Shugaban Najeriya ya yi Mummunan hatsari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da dan sa,  Yusuf Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da dan sa, Yusuf Buhari. Pulse.ng

Rahotanni daga Najeriya sun ce dan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi hadari a babur daren jiya a Abuja, kuma ya samu munanan raunuka a jikin sa.

Talla

Jaridar Daily Nigerian da ake wallafawa daga Abuja ta jiyo wata majiya daga fadar shugaban kasar na cewar Yusuf Buhari ya gamu da hadarin ne lokacin da suke tsere akan babur da abokin sa, abinda ya yi sanadiyar hadarin.

Jaridar ta ce, bayan karairayar da Yusuf ya yi, ya yi kuma doguwar suma, abinda ya sa aka ruga da shi asibitin Cedarcrest da ke Abuja.

Jaridar ta rawaito cewar ana kokarin fitar da Yusuf kasashen waje domin samun magani.

Sanarwar fadar gwamnati mai dauke da sa hannu kakakin shugaban kasar Garba Shehu ta ce Yusuf na samun sauki bayan an yi masa tiyata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI