Isa ga babban shafi
Boko Haaram

Shekau ya sake fitar da sabon bidiyo

Shugaban kungiyar Boko Haram a sabon hoton bidiyon da ya fitar a ranar Talata
Shugaban kungiyar Boko Haram a sabon hoton bidiyon da ya fitar a ranar Talata Yahoo.com
Zubin rubutu: Abdurrahman Gambo Ahmad
1 min

Ƙungiyar Boko Haram ta fitar da sabon bidiyo a wannan Talata, in da shugabanta, Abubakar Shekau ya yi ikirarin ƙaddamar da hare-hare na baya-bayan a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Talla

A karon farko kenan cikin ƴan watanni da Shekau ke fitar da sabon bidiyo a daidai lokacin da gwamnatin Najeriya ke ikirarin murƙushe mayakan.

A cikin bidiyon mai tsawon minti 31, Shekau ya ce, suna cikin ƙoshin lafiya kuma babu abin da ya same su.

“Dakarun Najeriya, ƴan sanda da wadanda ke mana zagon kasa ba za ku iya mana komai ba, kuma ba za ku samu ribar komai ba”in ji Shekau.

A cewar jagoran na Boko Haram, mayaƙansa ne sauka kai hare-hare a Maiduguri da Gamboru da kuma Damboa.

Bidiyon ya kuma nuna hoton harin ranar bikin Kirismati da aka ƙaddamar kan sojoji a wani wurin shingen binciken ababawan hawa a kauyen Molai da ke wajen birnin Maiduguri. Sai dai tuni sojoji suka ce, sun dakile harin.

A cikin watan Disamba, Boko Haram ta kai farmaki kan ayarin sojoji, yayin da ta baza ƴan kunar baƙin wakenta a wasu kasuwannni masu cike da hada-hadar jama’a a wasu birane da ke yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Akalla mutane 50 ne suka rasa rayukansu a cikin watan Nuwamba bayan wani dan ƙunar bain wake ya tarwatsa kansa a wani Masallaci da ke jihar Adamawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.