Najeriya

Malaman makarantun jihar Kaduna sun soma yajin aiki

Kungiyar malaman makarantun Firamare da Sakandare na jihar Kaduna NUT, ta fara yajin aikin sai baba ta gani, don tilastawa gwamnatin jihar janye matakinta na korar malamai kusan dubu Ashirin da biyu saboda rashin kwarewa.

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El Rufa'i.
Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El Rufa'i. Safari News Nageria
Talla

Malaman sun tsunduma yajin aikin ne duk da cewa gwamnatin jihar ta Kaduna, ta yi gargadin korar duk wani malami da ya goyi bayan matakin.

A cikin watan Nuwamban shekarar da ta gabata ne, gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da cewa akalla malamai dubu ashirin da daya da dari bakwai suka fadi jarrabawar da ta tsara musu a watan Oktoban shekarar 2017, daga cikin malaman makarantun dubu Talatin da uku.

Yayin zantawar sa da RFI Hausa Comrade Nasir Kabir sakataren gudanarwar na gamayyar kungiyoyin Kwadagon Najeriya ya ce zasu ci gaba da daukar matakan da shari’a ta bada dama wajen tilastawa gwamnatin Kaduna janye matakin nata.

Kwamared Kabir ya ce zasu tabbatar da samun goyon sauran kungiyoyin ma’aikatu wajen cimma burin da suka sanya a gaba na dakatar da korar malaman makarantun.

Shi kuwa shugaban kungiyar malaman makarantun ta NUT na karamar hukumar Zaria da ke jihar ta Kaduna, Malam Yahya Abbas, ya ce tilas ce ta su tsunduma cikin yajin aikin, saboda rashin sauraron kire-kirayen da suka yi wa gwamnati.

Malam Abbas, ya jaddada matsayarsu kan sabawa dokokin kwadago da matakin korar malaman ya yi, saboda mafi akasarin malaman sun samu makin jarrabawar sama da kashi 60.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI