Burtaniya-Faransa

Burtaniya za ta aika da jiragen yaƙi zuwa Mali

Jiragen yaki na soji.
Jiragen yaki na soji. AFP PHOTO / SIRPA

Burtaniya ta amince za ta aika da jirage masu saukar ungulu zuwa Mali domin taimaka wa dakarun Faransa wajen yaƙi da ayyukan ta'addanci a yankin Sahel na nahiyar Afirka.

Talla

Wannan mataki na da muhimmanci kasancewar ƙasar ta Faransa na da rauni a wannan fanni, kuma ana kallon hakan a matsayin mafari na kai irin wannan ɗauki a yankin.

An cimma wannan yarjejeniya ce a taron da Firaministan Burtaniya Theresea May da takwaranta na Faransa Emmanuel Macron suka gudanar ranar Alhamis a ƙasar ta Burtaniya.

A nata ɓangaren, Faransa za ta samar da dakaru waɗanda za su tallafa wa dakarun ƙawance na NATO da Burtaniya ke wa jagoranci a ƙasar Estonia.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.