Najeriya

Kaduna:Ƴansanda na musamman na aikin ceto Turawa

'Yansandan Najeriya.
'Yansandan Najeriya. AFP PHOTO / Quentin Leboucher

Rundunar ƴansanda a jihar Kaduna da ke tarayyar Najeriya ta kafa runduna ta musamman domin ceto wasu ƙwararrun turawa 4 kan samar da makamashi ta hanyar hasken rana da aka yi garkuwa da su a jihar, wadda ke yankin arewacin ƙasar.

Talla

Hukumar ta ce ƴansandan da aka kawo domin ceto turawan sun samu horaswa ta musamman kan dabarun shawo kan matsalar satar mutane da kuma dabarun magance ayyukan assha.

Ranar Talata ne aka sace Turawan ƙasashen Canada da Amurka yayin da suke kan hanyar su ta komawa Abuja daga garin Kafanchan da ke yammacin jihar.

Kaduna, jiha ce da ta yi kaurin suna kan sace-sacen al’umma, da rikici tsakanin kabilun musamman a kudancin jihar, amma jami’an tsaro da kuma gwamnatin kasar sun sha faɗin cewa suna ɗaukan matakai na kawo karshen al’amarin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.