Najeriya

EFCC ta bayar da belin Babachir Lawal

Tsohon sakataren gwamnatin Najeriya Babachir Lawal.
Tsohon sakataren gwamnatin Najeriya Babachir Lawal. AFP

Hukumar yaki da cin hanci da Rashawa ta Najeriya, EFCC, ta bayar da belin tsohon sakataren gwamnatin kasar Babachir Lawal.

Talla

Hukumar ta saki Babachir ne bayan shafe kwanki biyu da ya yi tsare a hedikwatarta da ke Abuja, inda ta ce tsohon sakataren gwamnatin yana bata hadin kai dangane da bayanan da ta ke nema daga gare shi.

A watan Oktoban shekarar da ta gabata ne, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kori Babachir Lawal daga aiki, bayan gamsuwa da kammala binciken kwamitin da aka kafa, kan zargin sa da karya dokar kasa wajen bai wa kamfaninsa kwangilar cire ciyawa a jihar Yobe a kan kudi Naira miliyan 200.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.