Najeriya

Na gaji da wannan masifar- Abubakar Shekau

Shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau
Shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau AFP PHOTO / BOKO HARAM

Shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau ya fitar da wani sabon sako na bidiyo, in da yake cewa ya gajji da masifar da suke fuskanta kuma ya gwammace mutuwarsa don hanzarta shiga aljanna.

Talla

A cikin sakon bidiyon na harshen hausa kuma na minti 10, Shekau ya bayyana matukar takaicinsa kan yadda ake kashe ‘yan kungiyarsa kuma ya ce, hakarsa ba ta cimma ruwa ba.

Babu dai alamar karsashi da ya saba nunawa a bidiyon da yake fitarwa, kuma muryarsa na nuna cewa ya karaya matuka saboda yadda sojin Najeriya ke samun nasara akan ‘yan kungiyarsa.

Wasu ‘yan kungiyar ta Boko Haram sun fito a matsayin dogaransa a sabon bidiyon, in da suke rike da bindigogi.

Yayi ta kokarin nanata cewa yana nan daram a dajin Sambisa a labe, kuma ya nemi ‘yan kungiyarsa da zage dantse don ci gaba da yaki.

Jagoran na Boko Haram ya ce, karya sojin Najeriya ke yi cewa, sun share su daga dajin Sambisa kuma suna nan da karfinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.