Bakonmu a Yau

Ana Tantance Yawan Dalibai Mata Da Suka Bace Bayan Harin Boko Haram A Makarantar Mata A Yobe

Sauti 03:16
Wasu 'yan matan sakandaren Chibok da aka sace kuma aka kubutar da su
Wasu 'yan matan sakandaren Chibok da aka sace kuma aka kubutar da su rfi

Rahotanni daga garin Dapciya dake jihar Yobe a Najeriya na cewa yau Talata jami'an Gwamnatin jihar da rakiyar jami'an tsaro suke  tantance irin hasarar da aka samu sakamakon hari da ‘yan Boko Haram suka kai yammacin jiya.A makarantar Sakandaren ‘yan mata dake garin  an gaza tantance adadin ‘yan mata da aka sace, sai dai an sami wasu ‘yan matan da suka sami raunuka a lokacin da suke tserewa zuwa daji, wasu kuma macizai  suka sare su.Garba Aliyu Zaria ya tattauna da Malam Dawanu Bula dake garin na Dabciya game da halin da ake ciki.