Najeriya

Majalisar Dinkin Duniya ta maido da ayyukanta a Rann

Wasu jami'an agaji na Majalisar Dinkin Duniya a filin jiragen sama na Maiduguri, yayin da suke janye ayyukansu daga garin Rann bayan harin Boko Haram, wanda uku daga cikinsu suka hallaka. Maris, 2, 2018.
Wasu jami'an agaji na Majalisar Dinkin Duniya a filin jiragen sama na Maiduguri, yayin da suke janye ayyukansu daga garin Rann bayan harin Boko Haram, wanda uku daga cikinsu suka hallaka. Maris, 2, 2018. OCHA/Yasmina Guerda/REUTERS

Ofishin bada agajin jinkai na Majalisar Dinkin Duniya OCHA, ya sanar da komawa bakin ayyukansa a garin Rann na jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Talla

Sai dai Ofishin na OCHA ya ce ma’aikatan nasa ba wai zasu rika kwana ba ne a garin na Rann ba, kamar yadda suke a baya, har sai an tabbatar da cikakken tsaro a yankin.

A ranar 2 ga watan Maris, Majalisar Dinkin Duniya ta janye ilahirin jami’anta daga garin na Rann, bayan Farmakin da mayakan Boko Haram suka kai ranar 1 ga watan, inda suka kashe mutane 8 ciki harda jami’an agaji 3 suka kuma sace ma’aikaciya jiyya 1.

Akalla mutane 80,000 jami’an agaji na majalisar Dinkin Duniya dana sauran kungiyoyi suke lura da su a garin na Rann da ke jihar Borno.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.