Najeriya

Fadar Buhari ta mayar wa Obasanjo sabon martani

Shugaba Muhammadu Buhari da Olusegun Obasanjo da kuma tsohon shugaban kasar a mulkin soja, Janar AbduSalam Abubkar, a birnin Addis Ababa na Habasha
Shugaba Muhammadu Buhari da Olusegun Obasanjo da kuma tsohon shugaban kasar a mulkin soja, Janar AbduSalam Abubkar, a birnin Addis Ababa na Habasha Femi Adesina/Facebook

Fadar gwamnatin Najeriya ta mayar da martani ga tsohon shugaban kasar, Olusegun Obasanjo da ya sake caccakar salon jagorancin shugaba Muhammadu Buhari a cikin wannan makon.

Talla

Fadar Buhari ta ce, ba za ta yi sa-in-sa da Obasanjo ba wanda ya kwatanta gwamnatin Buhari da gazawa a yayin jawabinsa a gaban dandazon wasu matasa da suka kai masa ziyara a birnin Abeokuta da ke jihar Ogun.

Obasanjo ya kuma bukaci gwamnatin APC da ta daina korafi kan tarin kalubalen da ta tarar bayan darewa kan karaga.

"Abin da muke da shi a yanzu shi ne gazawa, babu yadda za a karfafa gazawa, gazawa dai gazawa ce, da a ce akwai kwararriyar gwamnati mai aiki, da harkokin kasuwancin wasu daga cikinku sun habbaka a yau.” In ji Obasanjo.

Mai bai wa shugaban kasa shawara kan Harkokin Yada Labarai, Femi Adesin ya ce, tuni Ministan Yada Labarai da Al’adu, Lai Mohammed ya mayar wa Obasanjo martani a caccakar da ya yi wa gwamnatin Buhari a can baya, kuma babu wani sabon abu da ya fada a sabuwar caccakarsa.

Adesina ya kara da cerwa, gwamnatin APC za ta ci gaba da bada misali da irin gazawar tsohuwar gwamnatin da ta shude don ganin hakan bai sake aukuwa nan gaba ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI