Isa ga babban shafi
Najeriya

Majalisar Najeriya za ta amince da kasafin 2018 a makon gobe

Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Bukola Saraki da Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari da kuma shugaban Majalisar Wakilan kasar, Yakubu Dogara
Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Bukola Saraki da Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari da kuma shugaban Majalisar Wakilan kasar, Yakubu Dogara guardian.ng

Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Bukola Saraki da na Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara sun bayyana yiwuwar amince wa da kasafin kudi na 2018 nan da makon gobe bayan wata ganawa da suka yi da shugaba Muhammadu Buhari a wannan Litinin.

Talla

Shugabannin biyu sun yi ganawar ta sirri da Buhari a fadarsa ta Aso Rock da ke birnin tarayya Abuja a wannan Litinin, in da suka shafe tsawon minti 30 suna tattaunawa.

A yayin zantawa da manema labarai bayan ganawar, Saraki ya ce, suna fatan za a kaddamar da kasafin kudin a cikin wannan makon kafin amincewa da shi a makon gobe.

Wannan dai na zuwa ne bayan cika watanni 6 da Buhari ya gabatar da kasafin kudin ga Majalisar kasar, amma har yanzu Majalisar ta kasa amince da shi, lamarin da ya haifar da matsaloli da dama da kuma hana aiwatar da harkokin gwamnati.

Tuni 'yan Najeriya suka fara cece-kuce kan abin da suka kira zagon kasar da Majalisar ke yiwa bangaren zartarwa kamar yadda za ku ji a rahoton da wakilinmu Muhammad Kabir Yusuf ya aiko mana daga Abuja.

Cece-kuce game da tsaiko kan kasafin 2018 na Najeriya

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.