Isa ga babban shafi
Najeriya

Satar fasaha na durkusar da masana'antar fim a Najeriya-Popo

Osita Iheme da aka fi sani da Popo na daga cikin fitattun jaruman Nollywood a Najeriya
Osita Iheme da aka fi sani da Popo na daga cikin fitattun jaruman Nollywood a Najeriya RFIhausa/Bashir Ibrahim
Zubin rubutu: Abdurrahman Gambo Ahmad | Bashir Ibrahim Idris
Minti 2

Yayin da masu shirin fina-finan Najeriya ke ci gaba da daukaka sunan kasar a idon kasashen duniya wajen aikin su, daya daga cikin matsalolin dake ci musu tuwo a kwarya, itace matsalar satar fasahar jama’a. Sau tari wadannan mutane kan tarar da an kai fina finansu kasuwa ana sayar da su, kafin su fidda wadanda suka yi, matsalar da ke haifar musu da asara.

Talla

Wannan matsalar dai ba sabuwar aba bace a fadin duniya, ganin yadda ko a kasashen da suka ci gaba ake fama da ita.

Matsalar na ci gaba da haifar wa masu shirin fina-fina a Najeriya koma baya, musamman ganin yadda suke tafka asara bayan sun kashe makudan kudade wajen shirya fina-finan.

Osita Iheme da aka fi sani da Popo, wanda ya ziyarci ofishin RFI Hausa a cikin wannan mako ya ce "Lallai matsala ce babba da muke ci gaba da yaki domin ganin mun samu nasara. Muna ci gaba da zama da ita domin ba za ta hana mu aikin da muke yi ba."

"Muna rokon gwamnati da ta tashi tsaye wajen aiwatar da dokokin da aka shimfida wajen satar fasahar jama’a saboda matsalar na shafar masu shirya fina-finai da masu zuba jari da kuma jarumai, babu dadi da zaran ka kammala shirinka, kana bukatar samun riba kan dukiyar da ka kasa, kafin ka kyafta ido sai ka ga fina-finanka a kasuwa saboda yadda ake satar fasahar jama’a." In ji Iheme.

Osita  wanda aka fi sani da Popo ya ce, basu da karfin shawo kan wannan matsala ba tare da taimakon hukuma ba, in da ya roki gwamnatin Najeriya da ta tashi tsaye wajen kawo karshen satar fasahar al'umma.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.