Najeriya

Za mu hukunta masu kashe jama'a- Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya cika shekaru uku akan karagar mulkin Najeriyaa
Shugaba Muhammadu Buhari ya cika shekaru uku akan karagar mulkin Najeriyaa Sunday AGHAEZE / NIGERIA STATE HOUSE / AFP

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da ke cika shekaru 3 akan karagar mulki a wannan Talata, ya yi Allah–wadai da salwantar rayuka sakamakon tashe-tashen hankula tsakanin manoma da makiyaya, yayin da ya lashi takobin hukunta masu hannu a lamarin.

Talla

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a yayin gabatar da jawabi ta kafafaen yada labarai ga al’ummar kasar don tunawa da zagayowar ranar demokaradiya a Najeriya a yau Talata.

Shugaban ya ce, jami’an tsaro za su farauci masu laifi da masu daukan nauyinsu a tashe-tashen hankulan don fuskantar hukunci kamar yadda doka ta tanada.

Buhari ya ce, a yanzu “ Dukkanin matakai 3 na gwamnatin kasar na aiki da al’ummomi da kungiyoyin addinai don dawo da zaman lafiya tsakamin ‘yan Najeriya.

Har Ila yau, shugaban ya caccaki matsalar sace jama’a don karbar kudin fansa a sassan kasar, yayin da ya yi alkawarin amfani da doka don hukunta masu aikata wannan laifi.

Shugaba Buhari ya tabo batutuwa da dama da gwamnatinsa ta mayar da hankali akai da suka hada da tattalin arziki da cin hanci da rashawa da kuma tsaro.

Latsa alamar sautin da ke kasa don sauraren rahoto kan yaki da cin hanci da rashawa a gwamnatin Buhari.

Rahoto kan yaki da cin hanci a Najeriya

A bangare guda shugaba Buhari  ya ce, nan kusa zai sanya hannu kan sabuwar dokar rage shekarun cancantar tsayawa takarar neman mukaman siyasa, abin da ake ganin zai bai wa dimbin matasa damar shiga a dama da su a zaben shugabancin kasar a shekarar 2019.

A bara ne majalisun kasar biyu suka gabatar da kudirin dokar wadda ta bukaci rage shekarun cancantar tsayawa takarar shugaban kasa daga shekaru 40 zuwa 35, yayin da a bangaren gwamnoni da sanatoci aka bukatar rage shekarun daga 35 zuwa 30.

Sai dai a yanzu ana son takaita shekarun neman kujerar mamba a Majalisar Tarayya da ta Jiha zuwa 25.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.